Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana cewa babban dalilin da ya janyo rashin nasararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2015 shi ne cin amanar da wasu daga cikin kusa da shi suka yi masa, lamarin da ya bai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari damar yin nasara.
Jonathan, wanda ya bayyana haka yayin wani taro na tattaunawa kan dimokaradiyya da shugabanci, ya ce ya shiga zaben 2015 da cikakken kwarin gwiwa, amma daga baya ya fahimci cewa wasu daga cikin mutanen da ya fi dogaro da su sun bijire masa, abin da ya raunana matsayinsa a lokacin.
Ya kara da cewa, duk da haka ya amince da sakamakon zaben domin tabbatar da zaman lafiya da dimokaradiyya a Najeriya, matakin da ya ce ya kasance abin koyi ga shugabanni a kasashen duniya.
